'Yan Nigeria da satar shiga Africa ta Kudu da $10m

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma

Rundunar 'yan sanda a Afrika ta Kudu ta ce ta fara gudanar da bincike bayan da aka kwace wasu makudan kudade makare a cikin wasu jukunkuna daga hannun wasu 'yan Nigeria biyu da dan kasar Isra'ila guda da suka sauka a wani filin saukar jiragen sama da ke kusa da birnin Johannersburg.

A farkon wannan watan ne dai aka kwace kudaden, wuri na gugar wuri, da suka tasamma dola miliyan goma, daga hannun fasinjojijin wadanda suka sauka a cikin wani jirgin da ba na haya ba da ya isa kasar ta Africa ta Kudu daga Nigeria.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta Africa ta Kudu, Solomom Makgale, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewar rundunar ta fara gudanar da bincike a kan wannan al'amari amma kawo yanzu bata kama kowa ba.

Jami'an hukumar shigi da fici na Afrika ta Kudu ne dai suka gano kudaden, dola miliyan tara da dubu dari ukku, a cikin kayayyakin mutanen ukku da suka sauka daga wani jirgi wanda rahotanni suka ce ya tashi daga Nigeria ne ya sauka a filin saukar jiragen sama na Lanseria da ke arewa maso yammacin Johannesburg.

An boye kudaden ne a cikin wasu jikkuna guda ukku, kuma 'yan Nigeria'r biyu da dan Isra'ila guda sun bayyana cewar sun je da kudaden ne domin sayen makamai ga hukumar tattara bayanan sirri ta Nigeria.

Kafofin yada labarai na Africa ta Kudu sun fadi sunan dan kasar ta Isra'ila, amma basu bayyana sunayen 'yan Nigeriar biyu ba.

Image caption Mutanen sun saka kudaden a cikin jakunkuna

An ambato mai magana da yawun hukumar karbar haraji ta Africa ta Kudu, Marika Muller, ta na cewar an binciki mutanen ne bayan da jami'an shigi da fici suka tsan-tsamta da kayayyakin mutanen.

An dai karbe kudaden saboda sun zarta yawan abun da doka ta bari a shiga dasu zuwa kasar ta Africa ta Kudu, domin kuwa ba'a bayyana yawansu tare da shaidawa hukuma ba gabanin shiga da su.

Mai magana da yawun hukumar dake gabatar da kara ta Afrika ta Kudu, Nathi Mncube, ya ce bayanan da aka bayar akan abun da za a yi da kudaden suna cin karo da juna, kuma cike da suke da kura-kurai.