Boko Haram:Sojoji sun kara galaba a Konduga

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kungiyar Boko Haram ta kwace wasu garuruwa a Borno da Adamawa

Dakarun sojan Nigeria sun yi nasarar dakile wani harin ramuwar gayya da wasu mayaka wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai cikin daren jiya a garin Konduga na jihar Borno.

Rundunar sojin kasar ta ce 'yan kungiyar Boko Haram da dama ne suka mutu a arangamar, yayin da dakarunta ke bin sawun sauran 'yan bindigar da suka tsere dauke da raunuka.

Ko a makon da ya gabata ma, kungiyar Boko Haram ta kai hari kan garin na Konduga, inda rahotanni suka ce an kashe mayakan kungiyar da dama.

Wasu mazauna garin na konduga sun tabbatar da aukuwar harin na daren jiya, inda suka ce 'yan bindigar sun rabu ne zuwa ayari uku, amma dakarun sojan suka wargaza su.

Rundunar sojin ta ce dakarunta sun kwace motoci kirar Hillux guda uku da aka girka musu manyan bindigogi, da wata mota mai sulke guda daya, da sauran makaman yaki.