Tsoron Ebola ya hana Malamai komawa aiki

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Talata ne shugaban kasar ya bayyana cewa babu sauran mai fama da Ebola a Nijeriya

Kungiyar Malaman Makaranta a Nijeriya NUT ta umarci 'ya'yanta su yi biris da komawa aiki ranar 22 ga watan Satumba da gwamnatin kasar ta sanya, har sai ta ba su horon kare-kai.

Shugaban kungiyar, Michael Olukoya ya ce malamai ba za su koma aiki ba, har sai gwamnati ta ba su cikakken horo tare da samar musu kayayyakin kare kansu daga cutar Ebola.

Gwamnatin Nijeriya dai ta sanya Litinin mai zuwa a matsayin ranar komawa Makarantun kasar.

Tun da farko, an sanya 8 ga watan Satumba a matsayin ranar bude Makarantun Sakandare da na Firamaren kasar, amma sai aka dage zuwa 13 ga watan Oktoba kafin gwamnati ta rage wannan hutu.

Ministan lafiya na Nijeriya, Dr. Onyebuchi Chukwu ya ce an sanya ranar komawar ne bayan samun nasarar shawo kan cutar Ebola.