Ana zaman makokin mutuwar biri a India

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana kallon birin a matsayin abin bauta

Mutanen wani kauye a India suna zaman makokin mutuwar wani biri wanda suke tunanin mutuwar sa za ta iya janyo musu rashin sa'a.

Birin na daga cikin wasu birai da ke wajen ibada a Madhya Pradesh wadanda ake kallonsu a matsayin abin bauta.

An ga gawar birin ne a cikin wani wajen ninkaya a kauyen.

Dubban mutane ne suka yi bukin jana'izar birin kafin a kona gawarsa, sannan 'yan kauyen sun aske sumansu da kuma gemunsu a wani mataki na nuna alhini.