'Mun fito da gawarwaki 70 a cocin Lagos'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ginen da ya rushe wajen saukar baki ne

Hukumomi a Nigeria sun ce a halin yanzu an fiddo gawarwaki 70 daga cikin buraguzan ginin Cocin da ya fadi a Lagos ranar Juma'a.

Hukumar agajin gaggawa ta kasar-NEMA, ta ce an samu mutane 131 da suka tsira da ransu.

Tun farko Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya ce 'yan Afrika ta Kudu 67 ne suka mutu sannan wasu da yawa sun samu raunuka.

Mr Zuma ya ce adadin 'yan Afrika ta Kudu mafi yawa kenan da suka mutu a wani hadari daya tilo a wajen kasar a cbaya bayan nan.

Kungiyoyin coci-coci biyar daga Afrika ta Kudu ne ke ziyartar Cocin na Synagogue of All Nations a Najeriyar.