Nigeria: Ko zaben 2015 zai yiwu?

Hakkin mallakar hoto b

A Nigeria wata takaddama na kokarin tasowa game da batun da wasu 'yan majalisa suka taso da shi cewa, akwai yiwuwar rikicin Boko Haram ya hana gudanar da zaben shekarar 2015.

Mataimakin shugaban majalisar dattijaI, Ike Ekweremadu ya ce sashe na 135 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da damar a dage lokacin zabe matukar wani yanki na Nigeria na fama da yaki, kuma shugaban kasa ya yanke shawarar cewa ba za a iya gudanar da zabe ba.

Sanata Ali Ndume dan majalisar dattijai daga jihar Borno ya bukaci jama'a su kwantar da hankulansu saboda sashe na 135 na kundin tsarin mulkin bai bai wa shugaban kasa damar cewa ba za'a gudanar da zabe ba sai da amincewar majalisar dokoki.

Yace a matsayin su na wakilan jama'a za su yi abin da jama'a ke bukata ne.

Sanata Ndume yace sashen na 135 ya ba da dama ne kawai a yanayin da ake fama da rikici kuma ba za'a iya gudanar da zabe ba, shugaban kasa ya nemi karin watanni shida.

Yace burinsu shi ne a kawo karshen matsalolin tsaron da ake fama da su kafin zaben.

Karin bayani