2015: Baraka a PDP reshen Jigawa

Image caption Mr Jonathan na shan caccaka daga arewacin Nigeria

Wata babbar baraka ta kunno kai a jami'yyar PDP reshen jihar Jigawa game da batun zaben shugaban kasa a shekara ta 2015.

Wasu 'yan jam'iyyar PDP a jihar Jigawa da ke goyon bayan sake tsayawa takarar Shugaba Goodluck Jonathan sun fara mai da martani kan kalaman da gwamnan jihar ya yi cewa shi da magoya bayansa ba za su bi shugaba Jonathan ba idan ya yanke shawarar tsayawa takara a zaben 2015.

Shi dai Gwamna Sule Lamido ya ce gabanin zaben shekara ta 2011, shugaba Jonathan ya yi musu alkawarin wasu ayyuka a jihar domin su mara masa baya, amma har yanzu ba a cika musu ko da daya daga alkawuran ba, don haka 'yan jihar ba za su sake goya masa baya ba.

Sai dai tsohon dan majalisar wakilai daga jihar ta Jigawa, Alhaji Abba Anas Adamu a hirarsa da BBC ya ce suna goyon bayan takarar shugaba Goodluck a zaben mai zuwa, kuma Sule Lamido yana magana ne kawai a madadin kan sa.

Adamu ya ce "A tunani na akwai gyara a kai domin tsarin siyasa ba batun zuba adashi bane da kuma kwashewa. Saboda akwai wani bangaren adashi da shi (Sule Lamido) ya dauka wanda 'yan Nigeria sun sani."

Kawo yanzu Mr Jonathan bai ce zai tsaya takara a 2015 ba ko kuma a'a.