'Yan Afrika ta Kudu 67 sun mutu a Lagos

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Jacob Zuma ya nuna alhininsa

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya ce kimanin 'yan kasar 67 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka lokacin da ginin wani coci ya rushe a Legas a ranar Juma'ar da ta gabata.

A wata sanarwa, Mr Zuma ya ce wannan shi ne hadari mafi muni a tarihi da aka taba samun 'yan kasar masu yawa haka da suka mutu lokaci guda a wata kasar waje.

Wasu kungiyoyin coci-coci biyar daga Afrika ta Kudu suna ziyara a Synagogue Church of All Nations da ke Legas lokacin da sashen saukar baki na cocin ya ruguje.

Kawo yanzu dai ba a kaiga tantance adadin mutanen da suka mutu a lamarin ba, sai dai hukumomi a Nigeria sun ce mutane 62 ne suka mutu.

A ranar Talata, ma'aikatan agaji suka zakulo wata mace daga baraguzen ginin cocin da ranta amma ta samu raunuka.