Barcelona ta lashe wasan farko

Barcelona Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gerard Pique ne ya zirawa Barcelona kwallonta

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fara gasar cin kofin nahiyar turai da kafar dama, bayan da ta doke Apoel Nicosia da ci 1-0.

Dan wasanta Gerard Pique ne ya zira kwallon bayan da abokin wasansa Lionel Messi ya bugo masa kwallon, lamarin da ya basu damar doke zakarar ta kasar Cyprus a cikin minti na 28.

Sai dai a daya bangaren kuma abokiyar hamayyar dake rukuni daya da Barcelona, PSG ita kuma ta tashi da ci 1-1 da Ajax a birnin Armsterdam.

Edinson Cavani ne ya fara zirawa PSG kwallonta kana Lasse Schone ya farke cikin minti na 74.