2015: Jam'iyyar PDP ta ce sai Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo
Bayanan hoto,

Shugaba Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta amince da Shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takara daya tilo a zaben shekara ta 2015.

Majalisar zartarwar jami'yyar PDP ce ta yanke wannan shawarar a taron da ta gudanar a ranar Alhamis a Abuja.

Matakin ya nuna cewar babu wani dan takara da zai kalubalance Mista Jonathan a jam'iyyar PDP a shekara ta 2015.

'Ya'yan jam'iyyar ta PDP sun ce wannan matakin shi ne ya fi dacewa da jam'iyyarsu da kuma kasa baki daya.

Kawo yanzu Mista Jonathan bai bayyana ba a fili ko zai sake tsayawa takarar shugaban kasa ko kuma a'a.

A baya dai Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a wata hira da BBC ya ce shi da jama'arsa ba za su goyi bayan takarar Shugaba Jonathan a 2015 ba, sai ya cika wasu alkawarin da ya yi musu.

Sai dai kuma rahotanni sun ce bayan Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu na Jihar Neja ya sanar da cewa Mista Jonathan ne dan takarar jam'iyyar, ya bukaci Sule Lamido ya tabbatar da hakan, gwamnan na Jigawa kuma ya gyada kai yana nuni da amincewarsa.