Ebola: An sace liktoci da 'yan jarida a Guinea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane kusan 1,500 suka mutu sakamakon cutar Ebola a Yammacin Afrika

Rahotanni daga kasar Guinea na nuna cewa akwai yiwuwar an sace wasu ma'aikatan lafiya da kuma 'yan jarida da ke kokarin wayar da kan mutanen karkara.

Wasu mazauna wasu Kauyuka sun jefi wasu Likitoci uku da 'yan jarida uku da duwatsu a kauyen Wamey da ke kudancin kasar Guinea, a ranar Talatar da ta gabata.

Sai dai daya daga cikin 'yan jaridar ya samu kubuta.

A cewar Rahotanni an karya wata gada da gangan da nufin hana shiga kauyen.

Shugaban Bankin Duniya, JIM YONG KIM ya yi gargadin cewa annobar Ebola za ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba