An gano gawawwakin ma'aikatan lafiya a Guinea

Ma'aikatan lafiya a kasar Guniea
Bayanan hoto,

Ma'aikatan lafiya a kasar Guniea

Gwamnatin Guinea ta ce an gano gawawwakin ayarin ma'aikatan jinya da suka bace lokacin da suke aikin fadakar da jama'a akan cutar ebola.

An dai kai masu hari ne lokacinda da suke aiki a wani kauye a kudancin kasar.

Kasar Saliyo da ke makobtaka da Guinea na shirin hana zirga - zirgar mutane har na tsawon kwanaki uku domin dakile yaduwar cutar.

Hukumomi sun umarci mutane akan su tsaya a gida daga karfe goma sha biyu na daren alhamis har zuwa ranar lahadi.

Gwamnati kasar ta ce ana bukatar tsauraran matakai domin dakile cutar.