Na'urorin zamani kan haifar da hadura

Smartwatch
Image caption Amfani da na'urorin zamani yayin yin tuki na haddasa hadari

A Birtaniya, an gargadi matuka da su guji yin amfani da na'urorin zamani kamar agogo na Smartwatch yayin da suke yin tuki.

Kakakin hukumar dake kula da fannin sufurin kasar ya ce, za a hukunta wadanda aka samu da karya doka.

Akwai agogon hanu dake dauke da manhajoji da dama da kan iya baiwa mutum sukunin aika sakonni, wanda bayanai suka nuna cewa na daga cikin ababan dake janyo hadari yayin da masu ababan hawa ke kan hanya.

"Idan bayanan da aka tattara suka nuna cewa kana aika sako yayin tuki, hakan za ta hujja ce da za ta sa a hukunta mutum." In ji Kakakin.

Ya kuma kara da cewa har yanzu suna duba yuwuwar kara tsaurara dokar da za ta hana aikata wannan laifi.

"A watan Agusta mun kara yawan kudin tarar da ake cin mutum zuwa Euro 100, idan har aka samu mutum da laifin yin amfani da wata na'ura yayin da yake tuki." Ya kara da cewa.

Shi dai wannan hukunci za a aiwatar da shi nan take da an kama mutum, kamar yadda hukumomi suka nuna.

Ko da yake ba a haramta yin amfani da agogon smartwatch kwatakwata ba, amma idan har mutum ya wuce iri da gona ta hanyar yin tukin ganganci ko kasa sarrafa abun hawa ta dalilin yin amfani da wata na'ura, za a hukunta shi.

Masana da dama na da ra'ayin cewa akwai bukatar kamfanonin da suke samar da irin wadannan na'urori da su dinga jawo hankalin masu saya wajen ganin sun yi amfanin da na'uorin ta yadda ya kamata.