Ana jiran sakamakon kuri'a a Scotland

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana saran mutane za su fito kwansu da kwarkwata

Al'ummar yankin Scotland na Biritaniya suna jiran sakamakon kuri'ar raba-gardama da suka yi, bayan da kada kuri'ar ya zo karshe.

Ana kada kuri'ar raba-gardamar ne a yankin Scotland, a kan zabin da aka bai wa al'ummar yankin ko su ci gaba da kasancewa a karkashin Birtaniya, ko su balle.

A karon farko an kyale 'yan shekara goma sha shida zuwa sha bakwai su kada kuri'a.

Ana sa ran cewa sama da mutum miliyan hudu ne za su kada kuri'a, kuma da safiyar Juma'an nan ne ake sa ran sanar da sakamako.

Biritaniya dai ta kunshi yankuna ne guda hudu, wato Ingila, da Scotland, da Wales da kuma Ireland ta Arewa.

Shekara dari uku da bakwai dai aka kwashe ana zaman kasa guda tare da yankin na Scotland.