Yankin Scotland ba zai balle ba

Mutanen yankin Scotland sun yi watsi da yunkurin da wasu ke yi na a balle daga Birtaniya, inda kuri'u mafi rinjaye da aka kada na raba gardama suka nuna kin amincewa da hakan.

A yankuna da dama da ake sa ran masu so a balle daga Biratniya za su yi tasiri, rahotanni sun ce an samu gazawa wajen nuna goyon baya.

Wakilin BBC a yankin na Scotland, ya ce akwai alamu dake nuna cewa, gabanin kada kuri'ar mutane da dama sun canza ra'ayinsu bayan da watakila suka auna hadarin dake tattare da ballewar.

Ministan yankin , Alex Salmond, ya ce ya amince da shan kaye.

Ana sa ran fira ministan Birtaniya David Cameron zai gabatar da jawabi nan bada jimawa