Kamfanin Sony ya tafka asara

Kamfani Lataroni na Sony ya ce ya tafka asara fiye da yadda ya yi hasashe a cikin shekarar da mu ke ciki.

A yanzu kamfani ya ce yana tsamanin ya tafka asarar kudi fiye da yen biliyan 230 a maimakon dala biliyan hamsin.

Hakan ya biyo bayan koma baya da yake fuskanta a bangaren wayoyin salularsa sakamakon gogaya tsakaninsa da Apple da kuma Samsung.

A cikin wata sanarwar da kamfanin ya fitar ya ce a cikin tsarinsa na baya baya nan ya gano bakin zaren game da sauyin da aka samu a kasuwar wayoyin salula da kuma yadda ake gogaya.

Wanan shi ne karo na shida da kamfanin zai yi gargadi akan asarar da ya tafka , kuma ya sanar da hakan ne bayan da aka rufe kasuwar zuba hannayen jari ta Japan.

Sai dai masu sharhi akan al'maura sun ce yayinda kamfanin ke fuskantar rashin tabbas game da makomar wayoyinsa zai iya farfado da bangaren.

" Basu kadai ne kamfanin wayoyin tafi da gidanka da ke fuskantar matsi ba " a cewar Rachel Lashford daga kamfanin Canalys.

"Idan suka gudanar da sauye sauyen da ya kamata da kuma kayayakin da ake bukata,a farashi mai sauki , zasu iya samun cigaba."

Wakilin BBC kan tattalin arziki Andrew Walker ya ce kamfanin ya dade yana fama da matsaloli kuma ya yanke shawarar cewa ba zai biya masu zuba jari wani kaso ba.

Kamfanin ya ce zai rage yawan ma'aikatansa a sashin wayoyin salula da kashi goma sha biyar cikin dari a wani mataki na rage yawan kudaden da yake kashewa.

Sashin talibijin na Sony na fuskantar koma baya sai dai bangaren wasan komfutasa na samun tagomashi.