UEFA ta yi doka game da rauni a kai

UEFA
Bayanan hoto,

Dokar za ta baiwa alkalin wasa damar tsayar da kwallo na tsawon minti uku domin a duba dan wasa

Hukumar kwallon kafa ta UEFA ta samar da wata sabuwar doka kan yadda za a tunkari matsalar rauni a ka.

Sabuwar dokar ta baiwa alkalan wasa dama su tsayar da wasa na tsawon minti uku domin baiwa likitoci dama su tantance ko dan wasan da abin ya shafa zai iya ci gaba da buga kwallon.

A cewar hukumar ta UEFA hakan zai magance matsalar da 'yan kwallo ke fuskanta na shiga wani mawuyacin hali a duk lokaci da suka bugu a ka.

Dokar za ta fara aiki ne nan take.

Samar da wannan doka ya biyo bayan ci gaba da taka kwallo da wasu 'yan wasa biyu suka yi a lokacin gasar cin kofin duniya a Brazil.