Amurka na zargin China da satar bayanai

Amurka
Bayanan hoto,

Itama Amurka ta sha suka kan satar bayanan wasu kasashe

Amurka ta zargi gwamnatin China da shiga kwamfutocin wasu kamfanonin sufurinta domin satar bayanai.

A cewar hukumomin kasar ta Amurka, masu satar bayanan sun shiga na'urorin akalla sau 20 cikin shekara guda wadanda suka hada har da na wasu masu aiwatar da kwantiragi ga Amurkan.

Bayanai na cewa masu satar sun hari kwamfutocin ne dake dauke da bayanan yadda Amurkan ke jigilar dakarunta.

Daga cikin wuraren da aka abkawa, akwai wani jirgin ruwan kasar ta Amurka na fasinja, inda aka kwashi bayanai daga kwamfutocin jirgin, in ji majalisar dokokin kasar Amurka.

Sai dai gwamnatin China ta musanta wannan zargi.

An dai kwashe shekara guda ana gudanar da bincike kan wannan lamari, inda sai a watan Maris ne aka bayyana sakamakon a fili.

Sakamakon binciken har ila yau ya nuna cewa a cikin watanni 12 daga watan Yunin 2012, an samu hujjojin dake nuna cewa an shiga rumbun adana bayanai na masu kwantiragin sojoji sau akalla 50, ko da yake sakamakon bai bayyana wadanda abin ya shafa ba.

"Irin wannan kutsen satar bayanai a fannin da ya shafi tsaro, alama ce dake nuna dagewar da China ta yi wajen ganin ta bunkasa fannin harkar sadawar ta na zamani." In ji Sanata Carl Levin dake majalisar dokokin kasar.

Tuni dai ofishin jakadancin China dake birnin Washington ya musanta wannan zargi wanda ya kwatanta a matsayin wani abu da bashi da tushe.

Takaddama tsakanin Amurka da China kan batun satar bayanai, ba sabon abu bane, inda a baya ma Chinan itama ta zargi wasu masu leken asirin Amurkan da laifin kwasar wasu bayananta.