Kare bayanan sirri a Google da Apple

Google
Bayanan hoto,

Mutane da yawa basu san akwai hanyoyin kare bayanansu na sirri a jikin wayoyinsu ba

Kamfanin Google ya ce zai tsaurara matakan kare bayanan sirri na mutane a sabuwar wayar salula ta Android L da zai fitar.

Wannan mataki a cewar kamfanin, zai kara sa yunkurin da masu satar bayanan sirri ke yi ya zama lamari mai wuya ko kuma mika bayanan ga jami'an tsaro.

Haka kuma kamfanin Apple shima ya ce sabon shirinsa na iOS8 zai kasance dauke da wasu matakan kare bayanan sirrin jama'a ta yadda su kansu kamfanin ba za su iya ganin bayanan ba.

Sai dai damuwar itace, duk da cewa kamfanoni na kokarin samar da hanyoyin kare bayanan masu amfani da kayayyakinsu, da yawa daga cikin mutane ba sa amfani da hanyoyin kare bayanan ko kuma basu ma san akwai su ba.

A farkon makon nan ne, shugaban kamfanin Apple, Tim Cook, ya aike ta sakon intanet yana mai kara tabbatarwa masu amfani da kayayyakinsu cewa an saka matakan tsaro a bayanan sirrinsu.

"Ganin cewa muna da dumbin kwastomomi hakan ba zai sa mu shagala mu yi sakaci da kare bayanan sirrinsu ba." In ji Cook.

Ya kuma kara da cewa ba bu yadda za a yi suyi kasuwanci da bayanan sirrin mutane da suka zuba a wayoyinsu na iPhone ko kuma na iCloud.

A bangaren Google, kamfanin shima ya kara jaddada kudirinsa na kare bayanan sirrin jama'a inda ya ce ya kwashe sama da shekaru uku yana hakan.

"Sama da shekaru uku Android na kare bayanan sirrin jama'a, sannan mabudin bayanan ba a adana su a wani wuri da ya wuce cikin na'urar, saboda haka, zai yi wuya jami'an tsaro su samu bayanan." In ji Kakakin Google.