IS ta sako 'yan Turkiya su kusan 50

Asalin hoton, AP
Mayakan kungiyar ISIS
Fira ministan kasar Turkiya Ahmet Davutoglu ya ce kungiyar IS mai da'awar kafar daular musulunci ta sako wasu'yan Turkiya su 49 da take garkuwa da su.
A cewar Mr Ahmet, cikin wadanda aka sako akwai jami'an diplomasiyya da sojoji dama yara kanana.
Ya kuma kara da cewa tuni suka isa garin Sanliurfa dake kudancin kasar.
A dai watan Yunin da ya gabata ne 'yan kungiyar ta IS ta yi garkuwa da mutanen, bayan wani harin da suka kai a ofishin jakadancin kasar ta Turkiya dake birnin Mosul.
Turkiya ta rika dari -darin samar da sojoji da zasu dafawa matakin da Amurka ta dauka akan kungiyar IS dake fafutukar kafa daular musulunci a Iraki da kuma Syria saboda damuwar da aka nuna akan 'yan kasar da kungiyar IS ke garkuwa dasu
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti daya da BBC Safe 20/01/2021, Tsawon lokaci 1,14
Minti Ɗaya da BBC na Safiyar 20/01/2021 wanda Sani Aliyu da Nabeela Mukhtar Uba su ka karanto.