'Na ji dadin karamcin da PDP ta yi mini'

Mr Jonathan zai fuskanci kalubale kan wannan yunkurin
Bayanan hoto,

Mr Jonathan zai fuskanci kalubale kan wannan yunkurin

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya ce ya ji dadin karamcin da jam'iyyar PDP ta yi masa na amincewa da shi a matsayin dan takara daya tilo a zaben shekara ta 2015.

Shugaban kasar ya ce wannan karamcin da jam'iyyar ta yi, bisa goyon bayan gwamnonin PDP ya nuna cewar akwai bukatar ya rubanya ayyukan da ya ke yi a kasar.

Mr. Jonathan ya ce "Amincewa da ni a matsayin dan takara tilo ya nuna cewa akwai bukatar mu sake zage damtse domin kada mu ba da kunya."

A ranar Alhamis ne majalisar zartarwa ta jami'yyar PDP ta yanke shawarar amincewa da Mr. Jonathan a matsayin dan takarar da babu wanda zai yi hamayya da shi.

Wasu 'yan jam'iyyar PDP sun nuna rashin amincewarsu da wannan matakin, kuma rahotanni sun ce tuni har wani jigo a jam'iyyar ya shirya kalubalantar matakin a kotu saboda a cewarsa Shugaba Jonathan bai cancanci tsayawa takara a shekara ta 2015 ba.