'Yan Afrika ta Kudu 84 ne suka mutu a Lagos

Mujami'ar TB Joshua na da mabiya sosai a ciki da wajen Najeriya
Bayanan hoto,

Mujami'ar TB Joshua na da mabiya sosai a ciki da wajen Najeriya

Yawan 'yan kasar Afrika ta Kudu da suka mutu a masaukin bakin mujami'ar TB Joshua da ya rushe a jihar Lagos a Nigeria sun karu zuwa 84.

An dai yi amanna cewa 'yan Afrika ta Kudu da ke cikin ginin a lokacin da ya rushe sun kai 349.

Rahotanni sun ambato Jakadan Afrika ta Kudu a Najeriyar na cewa akwai yiwuwar yawan wadanda suka mutu ya zarta hakan.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne katafaren ginin masaukin bakin ya rushe a jihar Lagos da ke kudancin Najeriya.