'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara

Nijeriya
Bayanan hoto,

Mutane da dama sun tsere daga garin Hilinga zuwa makwabtan garuruwa

A Najeriya rahotanni daga jihar Zamfara na cewa wasu 'yan bindiga sun kashe akalla mutane biyu sun kuma raunata wasu da dama tare da kwace shanu a garin Hilinga da ke cikin karamar hukumar Maradun.

Wannan lamari ya faru ne mako guda bayan wani makamancin wannan hari da ya faru a wani gari dake kusa da garin.

Rahotanni na kara cewa jama'ar garin da dama sun tsere zuwa garin Isa na jahar Sokkwoto mai makwabtaka da yankin.

Malam Abubakar wanda da ya rasa kawunshi da kuma kannansa a cikin harin ya shaidawa BBC cewa da 'yan bindigar sun kai harin ne a jiya juma'a a garin na Hilinga.