'Yan sandan Nigeria sun musanta zargin Amnesty

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Amnesty ta zargi jami'an tsaron da take hakkin bil'adama
Bayanan hoto,

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Amnesty ta zargi jami'an tsaron da take hakkin bil'adama

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta musanta rahoton da kungiyar Amnesty International ta fitar da ke cewa jami'an tsaron kasar na cin zarafin bil'adama.

Kakakin rundunar, Emmanuel Ojukwu ya shaida wa BBC cewa ba gaskiya ba ne cewa 'yan sanda na cin zarafin wadanda ake zargi ta hanyar cire musu farata ko hakora ko yi wa mata fyade.

Rundunar ta ce tun bayan shekarar 1999 lokacin da kasar ta koma turbar Dimokradiyya, rundunar ta kara kyautata hanyoyin kare hakkokin bil adama.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce ana hukunta duk wani dan sanda da aka kama da laifin cin zarafin bil'adama a kasar.