Kungiyar ma'aikatan mai ta janye yajin aiki

Ministar mai ta Najeriya
Bayanan hoto,

Ministar mai ta Najeriya Alison Madeukwe

Ma'aikatan man fetur a Nijeriya da suka hada da 'ya'yan kungiyar NUPENG da PENGASSAN, sun janye yajin aikin da suka shafe kwanaki hudu suna yi a duk fadin kasar .

Kungiyoyin sun janye yajin aikin ne bayan da suka cimma matsaya da gwamnatin kasar a taron da suka yi a jiya akan harkar fansho na ma'aikatan kamfanin NNPC da kuma bukatar kyautata yanayin matatun man fetur na kasar.

Kungiyoyin sun ce gwamnatin kasar ta samin da biya da dama daga cikin bukatunsu.

A halin yanzu Nijeriya na sayo akasarin albarkatun man fetur dinta ne daga kasashen waje saboda matatun man fetur na kasar basa aiki yadda yakamata

Abin da wasu masu sharhi kan tattalin arziki suka ce na janyo illa ga tattalin arzikin kasar