Shugaban Oracle zai sauka daga mukaminsa

Shugaban Oracle Larry Ellison zai sauka daga mukaminsa bayan ya shafe shekaru 37 yana rika da ragamar shugabancin kamfanin..

An dai yi kiyasin cewa Mr Ellison shi ne na biyar a jerin manyan attajiran duniya kuma duk da cewa zai sauka daga mukaminsa na shugaban Oracle amma zai cigaba da tasiri a cikin harkokin kamfanin.

An bayanna Mr Hurd da kuma Madam Safra Catz a matsayin wadanda zasu gaji Mr Ellis.

Madam Catz za ta rika kula da sashin sarafa kayayaki da kudi da kuma harkokin da suka shafi sharia na kamfanin yayinda Mr Hurd zai rika kula da sashin cinikayya da kuma kasuwanci.

Mr Ellis me shekaru 70 na cikin mutane uku da suka kafa kamfanin a shekarar 1977 tare da Bob Miner da kuma Ed Gates.

Bayanan hoto,

Larry Elllis

A cikin watan sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce Mr Larry ya fito karar ya bayana anniyarsa na ciagaba da aiki a cikin kamfanin tare kuma da inganta fanin kimiya na kamfanin.

Mujjalar Forbes ta ce dukiyar Mr Ellison ta kai dala biliyan 51.3 inda ya mallaki kusan kaso ashirin da biyar na jarin kamfanin.

Mr Ellis ya kafa kamfanin Oracle ne da kudinsa da a loakcin ya kai dala dubu daya da dari biyu.