Scotland ta yi watsi da 'yancin kai

Scotland ta ce a'a
Bayanan hoto,

Scotland ta ce a'a

Yankin Scotland ya ka da kuru'ar ci gaba da zama a hadaddiyar daular Birtaniya, inda ya yi watsi da samun 'yancin kai da kashi goma cikin dari.

Jama'a masu dumbin yawa ne suka fito domin kada kuru'arsu a zaben raba gardamar da aka yi.

Masu yakin neman a ci gaba da zama tare sun samu nasara a yankunan da masu neman 'yanci suka yi zaton za su samu gagarumin goyon baya.

Shugaban masu neman a zauna tare, Alistair Darling, ya ce mutanen yankin Scotland sun zabi sauyi mai ma'ana a madadin rabuwar da ba'a bukata.

A lokacin da ya ke amincewa da shan kaye, minista na daya na yankin Scotland, Alex Salmond, ya ce kuru'ar ta nuna akwai gagarumin goyon baya na samun 'yan cin kai a nan gaba.

Amma Firayi Ministan Birtaniya, David Cameron, ya ce a yanzu an daidaita wannan magana baki dayanta a wannan takin.