'Ebola babban kalubale ne ga tsaro a Duniya'

Amurka ta yi alkawarin tura Sojojinta Yammacin Afrika domin yaki da cutar Ebola
Bayanan hoto,

Amurka ta yi alkawarin tura Sojojinta Yammacin Afrika domin yaki da cutar Ebola

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya ayyana cutar Ebola a matsayin babban kalubale da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.

Mambobin kwamitin 15, sun yi kira ga dukkanin kasashen duniya da su bayar da agajin gaggawa ga kasashen da cutar ta shafa a Yammacin Afrika.

Wannan dai shi ne karo na farko da Kwamitin tsaro na Majalisar ya yi irin wannan zama da ya shafi batun lafiyar al'umma.

Kusan mutane 2000 ne suka mutu sakamakon cutar ta Ebola, tun bayan barkewarta a Yammacin Afrika.