Ebola: Saliyo ta kafa dokar hana fita

Majalisar dinkin duniya ta ayyana cutar Ebola a matsayin babban kalubale na tsaro da zaman lafiya
Bayanan hoto,

Majalisar dinkin duniya ta ayyana cutar Ebola a matsayin babban kalubale na tsaro da zaman lafiya

Kasar Saliyo ta sanya dokar hana fita na tsawon kwanaki uku a yunkurin da takeyi na kawo karshen yaduwar cutar Ebola.

Dokar ta fara aiki ne a ranar Juma'a kuma za ta kare a ranar Lahadi mai zuwa, kuma a tsawon kwanakin jami'an sa kai za su bi gida-gida don gano masu dauke da cutar Ebola.

Haka kuma za a yi amfani da wannan dama wajen wayar da kan daukacin 'yan kasar miliyan shida a kan cutar, tare da raba musu sabulai.

Gwamnatin Saliyo ta ce akwai bukatar daukar kwararan matakai domin kawo karshen cutar ebola a kasar.