Masallacin da ke maraba da 'yan luwadi a Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Taj Hargey ya ce bai sabawa koyarwar musulunci ba

Wani Musulmi malamin jami'a ya bude wani Masallaci a kasar Afirka ta Kudu, wanda ya baiwa 'yan luwadi damar zuwa su yi sallah a masallacin.

Taj Hargey, ya ce Masallacin, wanda aka gina shi a Cape Town, yana maraba da kowa da kowa ba tare da la'akari da bambancin jinsi ko addini ba.

Taj Hargey, wanda Furofesa ne a cibiyar Nazarin Addinin Musulunci a jami'ar Oxford da ke Birtaniya ya shaida wa BBC cewa kowa na iya limanci a masallacin, har da Mata, don maza da mata na iya shiga sahu guda.

A yanzu haka, Furofesan na fuskantar barazanar kisa daga al'ummar da ke yankin.

Kungiyoyin Musulmi a kasar Afirka ta Kudu da kuma Majalisar shari'ar Addinin Musulunci ta kasar sun ce suna gudanar da bincike a kan sabon masallacin, kuma suna sane da korafin da al'ummar Musulmi ke yi a kansa.