Yaya Toure na bukatar taimako

Asalin hoton, AFP
Har yanzu Toure na fama da alhinin rasuwar dan uwansa
Kocin Manchester City, Manuel Pellegrini ya ce dan wasansa Yaya Toura na bukatar taimako daga kulob din domin ya ci gaba da haskawa kamar yadda ya saba.
Toure ya sha suka bayan da City ta sha kashi a hanun Bayern Munich da ci 1-0 inda aka soke shi kan rashin tabuka abin a zo a gani a karawar.
Yayin da Manchester City ke shirin fafatawa da Chelsea a ranar lahadi mai zuwa, Pellegrini ya ce Toure, mai shekaru 31 da haihuwa, zai farfado amma sai kulob din taimaka mai, kana ya yi nuni kan damuwar da ya ke ciki.
"Ya zama dole mu mara mai baya domin yana da muhimmanci a wasan da za mu yi a nan gaba" In ji Pellegrini.
Toure dai ya na fama ne da alhinin rasuwar dan uwansa a kwanan nan kamar yadda rahotanni suka nuna.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti Daya Da BBC Safe 18/01/2021, Tsawon lokaci 1,00
Minti Daya Da BBC Safe 18/01/2021