Yau za a kafa gwamnatin hadin gwiwa a Afghanistan

Afghan Canditates
Bayanan hoto,

'Yan takarar shugabancin Afghanistan

Mutane biyu da suka yi takarar mukamin shugaban kasa a Afghanistan za su hanu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin-gwiwa, idan an jima a yau

Yarjejeniyar ta zayana cewa Ashraf Ghani shi ne zai zama sabon shugaban kasar Afghanistan me karfin fada da ji yayinda wanda za'a nada a matsayin CEO wanda mukami ne kamar na firai ministan zai kasance karkashinsa .

Sai dai ba za'a rantsar da Mr Ashraf bayan an sanar da sakamakon zabe ba a maimakon haka mutane biyu zasu sa hanu ne kan yajejeniyar kafa gwamantin hadin giwa kafin a sanar da sakamakon zaben.

Haka kuma sabon mei rike da mukamin na CEO wanda Abdullah Abdullah ne ya bada sunnasa zai kasance kusa da shugaban kasa lokacin da za'a rantsar da shi.

Dr Abdullah ya samu damar nada manyan mukamai ne saboda shi da Asharf Ghani kowanensu na samun albashi iri daya .

Yarjejeniyar dai ta ce bangarorin biyu zasu samu wakilci na bai daya a matakin shugabanci