An tunzura masu amfani da Apple

Apple
Bayanan hoto,

Masu amfani da iPad da iPhone na Apple sun ta goge hotunan wayoyinsu

Masu amfani da iPhone da iPad na Kamfanin Apple sun nuna fushinsu bayan da kamfanin ya inganta fasalin wasu kayayyakinsa.

Hakan ya sa masu amfani da iPad da iPhone suka yi ta share hotuna da wasu manhajoji domin su samar da gurbin da zai amince da sabon canjin da aka samu wanda zai fito a iOS8 da ke bukatar sarari mai nauyin 5.8GB.

Mutane da dama sun shiga shafukan twitter da dandalin sada zumunta na Facebook suna bayyana fushinsu saboda wannan lamari.

Dama wasu masana sun bayyana cewa a duk lokacin da Apple ya yi irin wannan canji akan samu makamancin wannan matsala na dole sai masu amfani sun goge wasu shirye shiryensu.

"Wannan canji yana da amfani, amma idan dai ba za ka goge rabin shirye shiryen dake wayar ka ba." In ji David Roberts, wani mai amfani da Apple ya bayyana a shinfinsa na Tweeter.

Shi kuwa Daniel Zennon cikin barkwanci ya ce "wato Apple sun sa mutane sun saka wani shiri, sun kuma ce a cire saboda a samar da gurbi ga wani."

Wannan ba shine karon farko da aka sami irin wannan lamari ba.

A shekarar 2012 inganta nau'in wayar iOS6 ya sa wasu sun rasa shirye shiryen dake jikin wayarsu da dama.