Arsenal ta doke Aston Villa 3-0

Arsenal
Bayanan hoto,

Welbeck ya bude asusun zira kwallo a Arsenal

Kungiyar Arsenal ta samu nasara akan Aston Villa da ci 3-0 a gasar Premier.

Arsenal ta zira kwallaye ukun ne cikin minti hudu kuma Mesut Ozil ne ya fara bude raga bayan da Danny Welbeck ya garo mai kwallon.

Shima Ozil ya taimakawa Welbeck ya zira kwallonsa ta farko cikin wasanni 16 da ya bugawa kulob din.

Yanzu haka Arsenal ta buga wasannin 16 a Villa Park ba tare da an samu nasara a kanta ba.