West Ham ta mamayi Liverpool 3 -1

Liverpool
Bayanan hoto,

Liverpool ta rasa wasanni uku ke nan cikin guda biyar da ta buga

Liverpool ta sha kashi a hanun West Ham da ci 3-1 a karawar da suka yi a gasar Premier.

Wannan shine karo na uku da ake doke kungiyar ta Liverpool a wannan kakar wasa cikin wasannin biyar da ta buga.

Wisnton Reid da Diafra Sakho ne suka fara zirawa West Ham kwallayenta, kamin dan wasan Liverpool Raheem ya farke kwallo guda.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma Morgan Amalfitano ya kai yawan kwallayen West Ham zuwa uku.

Wannan itace nasarar farko da West Ham ta samu a wannan kakar wasa a cikin gida.