Boko Haram sun kashe mutane a Mainok

A Najeriya 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a garin Mainok da ke kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Rahotanni na sun ce akalla mutane 30 ne suka mutu a harin, galibinsu kuma farar-hula ne.

Wasu da aka yi abin a kan idanunsu sun ce 'yan kungiyar sun mamaye wata kasuwar kayan abinci ne a ranar Juma'a.

Ganau sun ce jami'an tsaro sun tsere lokacin da aka kai harin, amma wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa daga baya jami'an tsaron sun yi ta fafatawa da maharan har zuwa safiyar Asabar.

Kungiyar Boko Haram dai ta kwace iko na wasu garuruwa da ke kusa da Maiduguri da kuma wasu a arewacin jihar Adamawa a 'yan makonnin nan.

Sojojin Najeriya dai na fama da 'yan kungiyar, duk kuwa da dokar ta-bacin da aka sanya ma jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.