'Za mu murkushe 'yan bindiga a Zamfara'

Hukumomi a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce za su murkushe 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar.

Sun bayyana hakan ne bayan wani harin da 'yan bindiga suka kai a garin Hilinga ranar Juma'a.

'Yan bindigar sun kashe akalla mutane biyu sun kuma raunata wasu da dama tare da kwace shanu masu yawa a harin.

To amma hukumomi a jihar sun ce wani kwamiti na musamman wanda ya kunshi jami'an gwamnati da na tsaro na na kokarin shawo kan matsalar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Mohammed Birnin Magaji, ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa gwamnati na daukar matakan inganta tsaro a jihar.

Harin na ranar Juma'a dai ya faru ne mako guda bayan wani makamancinsa da ya faru a wani gari da ke kusa da yankin.

A yanzu dai haka jama'ar garin da dama sun tsere zuwa garin Isa na jihar Sokoto mai makwabtaka da yankin.