Ghani zai zama shugaban Afghanistan

Bayan shafe watanni ana takaddama, mutane biyun da suka yi takarar shugabancin kasar Afghanistan sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin-gwiwa.

A karkashin yarjejeniyar, Ashraf Ghani shi ne zai kasance shugaban kasa, yayin da Abdullah Abdullah aka ba shi damar zabo wanda za a nada wa mukamin shugaban gwamnati, watau kwatankwacin fira-minista.

Shugaban Afghanistan mai barin-gado, Hamid Karzai, ya halarci bikin sa-hannu, inda ya bayyana farin cikinsa ga tsarin.

Ya ce: "Ina matukar farin cikin cewa 'yan uwanmu guda biyu masu daraja, wato da Dr Ashraf Ghani da Dr Abdullah Abdullah sun daidaita da juna don ci gaban wannan kasar, ta hanyar kafa gwamnatin hadin-gwiwa.

"A madadin al'umar Afghanistan, Ina taya su murna da ganin wannan rana."