Ebola: Ana son a jinkirta bude makarantu

A Najeriya, kungiyar malamai ta kasar ta bukaci gwamnati da ta kara jinkirta batun komawar dalibai makaranta saboda cutar Ebola.

A ranar Litinin ne dai aka tsara dalibai za su koma makaranta, bayan dogon zaman da suka yi a gida, don hana yaduwar Ebola, wadda ta bulla a kudancin kasar.

Shugaban kungiyar malaman ya ce babu wani tanadi kariya da aka yi a makarantun.

Sai dai Shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan, ya yi watsi da kiran da kungiyar malaman ke yi.

Amma wasu jihohin da kuma wasu makarantu masu zaman kansu a kasar sun ce za su jinkirta komawar daliban.

A da dai gwamnatin tarayya ta ce ba za a bude makarantun ba har sai tsakiyar watan Oktoba, amma daga baya ta takaita lokacin, ta ce a koma a ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, bayan da ta lura cewa matsalar cutar Ebolar ta ragu sosai a kasar.