Limamai sun ba Jonathan zabi kan tsaro

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Malaman sun bukaci Shugaba Jonathan da ya tashi tsaye akan tabarbarewar tsaro

Kungiyar malamai da limamai a Nigeria ta bukaci shugaban kasar Goodluck Jonathan da manyan jami'an tsaro da su hanzarta magance matsalar tabarbarewar tsaro ko kuma su ajiye ayyukan su.

A wata ganawa da manema labarai ta musamman a Kaduna tare da hadin gwiwar kungiyar musulmi dalibai ta arewacin Najeriya, malamai da limaman sun nuna damuwa a bisa yadda gwamnati ke tunkarar batun hare haren ta'addanci a kasar.

Haka kuma malaman sun bukaci gwamnati da yiwa 'yan kasar cikakken bayanai dangane da wasu al'amurra da ke wakana a kasar masu nasaba da tsaron musamman batun wani jirgin sama daga Najeriya da aka kama dauke da kudade a Afurka ta Kudu.

Yankin arewacin Nigeria dai na fama da matsalar hare haren 'yan kungiyar Boko Haram wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dama dama.

Karin bayani