Bikin ranar zaman lafiya ta duniya

Ban  ki Moon
Bayanan hoto,

Sakatare janarar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon

A yau kasashen duniya ke bikin zaman lafiya na shekarar 2013.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta ware ranar 21 ga watan satumba na kowace shekara, domin fadakar da mutane akan muhimmanci zaman lafiya tsakanin alumma.

Taken bikin bana, shi ne "jama'a na da yancin samun zaman lafiya."

A jawabinsa game da bikin na bana Sakatare janarar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi kira kan a dakatar da bude wuta a duk kasashen dake fama da tashe tashen hankula.

Ya kuma nemi mayaka akan su ajiye makamansu domin samun zaman lafiya.

Mr Ban ya ce tashe tashen hankula na janyo matukar wahala ga iyalai da alumomi da kuma sauran kasashen duniya.

A shekarar 2001 Majalisar Dinkin duniya ta sanya ranar ashirin da daya ga watan satumba a matsayin ranar zaman lafiya ta duniya kuma taken bikin bana shi ne jama'a nada yancin a samun zaman