'Yan Boko Haram sun kai hari Amchide

Jami'an tsaro
Bayanan hoto,

Jami'an tsaro

Rahotanni daga garin Amchide na Kamaru mai makwabtaka da Banki a Najeriya na cewa an yi ta musayar harbe-harbe, har zuwa daren Litinin, tsakanin wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne da kuma jami'an tsaro na Kamaru.

Wasu mazauna garin sun ce bayan zuwan maharan ne sai mazauna garin suka bukaci agajin sojoji wadanda suka zo aka yi ta musayar harbe harbe.

Babu karin bayani game da wadanda rasa rayukansu ko suka jikkata.

Artabun da ake yi da'yan Boko Haram ya tilasta wa mutane gudun hijira daga wasu garuruwa na Nigeria.