Boko Haram ta kai hari garin Ldama a Cameroon

Asalin hoton, AFP
Kasashen Nigeria da Kamaru na fuskantar hare haren Boko Haram
Wasu da ake zargin 'Yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari ranar Lahadi a garin Ldama da ke kusa da Tourou a yankin arewa mai nisa a Cameroon.
Bayanai wadanda bana hukuma ba, na cewa an samu asarar rayukan jama'a sama da goma cikinsu har da wani jami'in tsaro guda.
Wannan harin da 'yan kungiyar Boko Haram suke kaiwa a iyakokin Cameroon da Nigeria na kara adadin 'yan gudun hijira da kuma masu kauracewa matsugunansu.
Kasashen Nigeria da Kamaru na fuskantar hare haren mayakan Boko Haram.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti Daya da BBC Safe 15/01/2021, Tsawon lokaci 1,07
Minti Ɗaya da BBC na Safiyar 15/01/2021, wanda nabela Mukhtar Uba da Sani Aliyu su ka karanto.