An soki eBay saboda kutsen da ake mushi

Masu kutse suna satar bayanan banki na masu cinikayya
Bayanan hoto,

Masu kutse suna satar bayanan banki na masu cinikayya

Wasu kwararrun masu bincike akan sha'anin tsaro na intanet sun bukaci kamfanin eBay da ya gaggauta daukan mataki na hana tallata wasu hajoji da masu kutsen satar bayanan jama'a keyi ta shafinsa na intanet.

Masu binciken suka ce matsalar, ta sa jama'a na cigaba da zama cikin hadari.

Kafar yada labarai ta BBC ta gano hajoji fiye da dari daya da aka kutsa su cikin shafin eBay domin yaudarar masu cinikayya ta yadda za a saci bayanansu batare da sanin su ba.

A ranakun karshen mako, wasu masu cinikayyar sun gana da BBC inda suka ce sunyi kokarin gargadin kamfanin eBay akan matsalar.

Kamfanin eBay ya ce zai cigaba da yin gyara akan shafinsa na intanet da duk kan abubuwwan da shafin ya kunsa.

Bayanan hoto,

Akasarin hajojin bogi da masu kusten ke tallatawa manyan wayoyin salula ne na talabijin

Kafar BBC ta gano cewa masu mu'amalar cinikayya da kamfanin eBay da dama sun fuskanci matsalar kutse a shafinsa na intanet, inda ake tallata musu hajoji na bogi, kuma da zarar sun nemi tayawa, sai a nadi bayanansu na banki zuwa wasu shafukan da ba na eBay ba.

Wani daga cikin mutanen da matsalar kutsen ta shafa ya ce ya kasa yin amfani da asusun siyayyarsa a eBay na dan wani lokaci, kuma daga baya aka caje shi Fam 35 akan wasu hajoji da bai siya ba.

Mafi akasarin hajojin da ake yaudarar mutanen da su a shafin eBay na Intanet sun hada da manyan wayoyin salula da talabijin da kuma tufafi.

James Lyne na kamfanin samar da tsaro na Sophos ya ce a yanzu, ba a san ainihin abinda masu kutsen suka kullata ba, amma dai tabbas ana karkatar da masu siyayya a eBay zuwa wasu shafuka na rashin gaskiya.

Kafar yada labarai ta BBC ta tabbatar da cewa tun a watan Fabuwairu ne kamfanin eBay ke fuskantar wannan matsala, ko da yake wasu kwararru sun ce matsalar ta na nan fiye da shekara daya.