Sabon kawance tsakanin Iran da Saudia

Asalin hoton, AP
Kasashen Iran da Saudi Arabia na fuskantar barazana guda a yanzu
Ministocin harkokin kasashen waje na Iran da Saudi Arabia sun gana a karon farko tun lokacin da aka zabi Shugaba Hassan Rouhani a bara.
An ruwaito cewa mutanen biyu sun gana ne a birnin New York na Amurka.
An ambato ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif yana cewa ganawar ka iya kasancewa wani sabon babi da zai bude wata sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu masu gaba da juna.
Iran mai bin mazhabar Shi'a da kuma Saudi Arabia mai bin mazhabar Sunni sun yi hannun riga a rikice- rikicen da ake fama da su da dama wadanda suka hada da na Syria da kuma Iraqi.
Kowacce kasa na son ganin ita ke da karfin fada aji a yankin gabas ta tsakiya.
Sai dai Kasashen biyu sun gano suna fuskantar barazana guda yanzu daga Kungiyar mayakan IS.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, MINTI ƊAYA DA BBC NA RANA 20/01/2021, Tsawon lokaci 1,14
MINTI ƊAYA DA BBC NA RANA 20/01/2021