'Yan majalisar dokoki sun bamu kunya'

Tabarbarewar tsaro na cigaba da jan hankalin gwamnonin Najeriya
Gwamnan jahar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya koka da matsalar tabarbarewar sha'anin tsaro da kuma yawaitar 'yan gudun hijira a Najeriya.
Gwamna Kwankwaso ya bayyana cewa 'yan majalisar dokoki da jama'a suka zaba wadanda ke Abuja sun ba da kunya.
Gwamnan ya ce 'maimakon su kare mutuncin mu da kuma darajar mu, sun koma wakiltar aljihunsu'.
Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya kuma ce ba daidai bane a dage zaben Najeriya kamar yadda wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya ke tunani sakamakon tabarbarewa tsaro.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, MINTI ƊAYA DA BBC NA RANA 19/01/2021, Tsawon lokaci 1,04
MINTI ƊAYA DA BBC NA RANA 19/01/2021