'Yan bindiga sun kai wa 'yan sanda hari a Kogi

Kungiyar Boko Haram ta sha kaddamar da hare hare a ofisoshin 'yan sanda a arewacin Nigeria
Bayanan hoto,

Kungiyar Boko Haram ta sha kaddamar da hare hare a ofisoshin 'yan sanda a arewacin Nigeria

Wasu 'yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda na Adogo dake karamar hukumar Ajaokuta a jihar Kogi.

Wata sanarwa da ta fito daga Shelkwatar 'yan sandan Nigeriar tace jami'anta sun maida martani ta hanyar budewa 'yan bindigar wuta wadanda suka yi kokarin awon gaba da makaman 'yan sandan.

Sanarwar tace an kone da kuma rushe wani bangare na ofishin 'yan sandan sakamakon harin 'yan bindigar.

Hukumar 'yan sandan Nigeriar ta kara da cewa babu wani jami'inta da ya jikkata, amma wasu daga cikin 'yan bindigar sun tsere da raunin harbin bindiga.

'Yan sanda sun tsaurara tsaro a yankin, kuma ana cigaba da yunkurin gano 'yan bindigar da suka tsere da raunin bindiga in ji sanarwar.