Microsoft ya jinkirta kaddamar da Xbox

 Xbox One

Asalin hoton, Microsoft

Bayanan hoto,

An shirya kaddamar da Xbox One ne don fara sayarwa a kasuwannin China a ranar 23 ga watan Satumba.

Kamfanin Microsoft ya soke bukin kaddamar da wasannin bidiyo na Xbox One a kasar China kwanaki biyu kafin ranar da aka shirya kaddamar da na'urar.

Tun da farko an shirya kaddamar da Xbox One ne don fara sayarwa a kasuwannin China a ranar 23 ga watan Satumba.

Sai dai Microsoft bai bayyana dalilan soke kaddamarwar ba, ko kuma sanar da wata rana da za a yi hakan a nan gaba.

Microsoft da Sony da kuma Nintendo na kokarin shiga kasuwannin China bayan da a watan Janairu aka dage haramcin sayar da wasannin kumfuta na kasashen waje da aka kwashe shekaru 14 ana yi.

Asalin hoton, Microsoft

Bayanan hoto,

Microsoft ya ce zai bukaci karin lokaci don samar da ingantattun na'urori ga abokan hulda

A wata sanarwa, Microsoft ya ce "duk da nasarorin da aka gani, zamu bukaci karin lokaci don samar da ingantattun na'urori ga abokan huldar mu".

Sai dai kamfanin ya ce za a kaddamar da wasannin bidiyon kafin karshen shekarar 2014.

Manajan kamfanin Microsoft a China, Enwei Xie ya ce duk mutanen da suka aike da bukatar sayen na'urar wadanda kuma su ke tsammanin a kawo musu a wannan makon za a basu gyara.

Idan aka fara sayar da na'urar, ana saran farashin ta za ta kai dala 600, ko kuma Fam 370.

Wannan jinkiri na kaddamar da na'urar na zuwa ne yayin da hukomomin kasar China ke binciken Microsoft bisa zargin kamfanin da keta wasu dokokin kasar.