Gidan tarihin London na wasan kwamfuta

Asalin hoton, Getty
Ana matakin farko na shirye shiryen kirkiro wasan kwamfuta na gidan adana kayan tarihi dake London
Za a bullo da wani sabon wasa na komfuta a cikin wasannin Minecraft, wanda za a kwaikwayi gidan adana kayan tarihi na Burtaniya da ke London tare da duk kan kayayyakin tarihi da ke cikinsa.
Aikin kirkirar gidan adana kayan tarihin a cikin wasannin Minecraft wani bangare ne na kokarin da gidan kayan tarihin ya ke yi na kara jan ra'ayin jama'a.
An kirkiri wasannin Minecraft na kwamfuta da dama masu kwaikwayon wasu ma'aikatu da suka hada da Ordinance Survey da kuma gwamnatin Denmark saboda matasa su kara fahimtar yadda ayyukan ma'aikatun ke gudana.
A cikin makon jiya aka sayar da manhajar wasa ta Minecraft ga kamfanin Microsoft akan kudi dala biliyan biyu da miliyan dari biyar.
Mai magana da yawun gidan adana kayan tarihin, ta ce har yanzu ana matakin farko ne na shirye-shiryen aikin kirkirar gidan tarihin a cikin wasannin Minecraft, domin ba a fara aikin ba.
Ta ce gidan tarihin ya na da niyyar daukan mutanen gari aiki su taya shi aikin.
Asalin hoton, Getty
Za a sanyan duk kan kayayyakin tarihi dake cikin gidan a cikin wasan kwamfutan
Wani ma'aikacin gidan adana kayan tarihin ya wallafa bayanai agame da aikin kirkirar wasan na kwamfuta ta shafin sada zumunci na Reddit, inda ya yi kira ga masu sa kai da su shiga cikin tsarin.
Matakin farko na aikin zai hada da gina daukacin gidan adana kayan tarihin a cikin kwamfuta, kamar yadda yake a zahiri.
Anan gaba hukumomin gidan adana kayan tarihin ke sa ran za a kammala matakin farko na aikin domin a samu gabatar da shi ga jama'a a ranar 16 ga watan October domin tafka mahawara akai.
Ed Barton, wani mai bincike akan wasannin kwamfuta ya shaidawa BBC cewa yunkurin sanya gidan adana kayan tarihin na Burtaniya cikin wasannin Minecraft zai sa jama'a su rika yi wa gidan kallon wani abin jin dadi, kuma zai zamo wani abin neman ilimi a tsakanin matasa.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti Ɗaya Da BBC Na Rana 22/01/2021, Tsawon lokaci 1,09
Minti Ɗaya Da BBC Na Rana 22/01/2021