'An shawo kan Ebola a Nigeria da Senegal'

Mutane 2,800 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola
Bayanan hoto,

Mutane 2,800 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce an shawo kan barkewar cutar Ebola a kasashen Nigeria da Senegal cikin kasashe biyar da cutar ta bulla a yammacin Afirka.

Amma WHO ta ce gabaki-dayan yawan mutanen da suka mutu sun karu zuwa kusan mutane 2,800.

A Kasar Saliyo, Shugaban cibiyar ayyukan gaggawa akan cutar Ebolan Stephen Gaojia ya ce an sami nasarar shawo kan cutar bayan da aka kawo karshen dokar hana fitar da aka sanya a Kasar a ranar Lahadi.

Hukumomin Kasar Saliyo sun sami mutane 130 dake dauke da cutar a lokacin da dokar ke aiki.